Gobara ta kone ofishin INEC a jihar Plataeu


Gobara ta kone ofishin hukumar zabe ta kasa, INEC dake karamar hukumar Qua’an ta jihar Plataeu kasa da mako guda gabanin babban zaben shugaban kasa na ranar Asabar.

Shugaban sashen hulda da jama’a da kuma ilmantar da masu kada kuri’a a hukumar zaben reshen jihar Plataeu, Osaretin Imahiyereobo ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin.

Jami’in ya ce wani megadi da yayi mankas da barasa shine ya haddasa tashin gobarar.

Imahiyereobo bai bayyana lokacin da gobarar ta fara ba sai dai ya ce gobarar a kawo cikas da shirye-shiryen babban zaben shekarar 2019 a karamar hukumar.

Ya bayyana cewa Ofishin ya kone tare da dukkanin abinda yake ciki na kayan zabe.


Like it? Share with your friends!

1
64 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like