Gobara ta kone kayan agajin yan gudun hijira a Borno


Wata gobara da safiyar ranar Laraba, ta kona kayan agaji na miliyoyin naira a wurin ajiye kayayyaki da kwamitin shugaban kasa a yankin arewa maso gabas ke amfani da shi, dake kan titin Baga a Maiduguri.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa gobarar ta kama ne da misalin karfe 06:00 na safe inda ta kone akalla katifu 400,mota da kuma wasu kayayyakin dake dakin a jiyar.

Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar, Civil Defence, ƴansanda da kuma mutanen gari sun yi gaggawar isa wurin inda suka takamaika wajen kashe wutar.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar,Ambursa Pindar ya ce an tura motar kashe gobara ya zuwa wurin.

“Baza mu iya gano musabbabin faruwar gobarar ba saboda babu kowa a wurin lokacin da lamarin ya faru, babu jami’an tsaro,babu kowa,” ya ce.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like