Gobara ta kone kasuwar yan katako ta Amu dake Legas


Kayayyaki da dukiya na miliyoyin naira ne suka kone bayan da wata gobara ta tashi da tsakar daren ranar Asabar a kasuwar yan katako ta Amu dake Mushin a birnin Legas.

Nosa Okunbor jami’in hulda da jama’a na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas LASEMA shine ya tabbatar da faruwar haka cikin wata sanarwa.

Ya ce an samu rahoton ta shin gobarar da misalin karfe 1:25 ta hanyar kiran kai daukin gaggawa da hukumar ta samu.

Ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa gobarar ta samo asali ne daga matsalar karuwar karfin hasken wutar lantarki kuma ba a samu asarar rayuka ba a gobarar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like