Gobara ta kone gidan mutumin da ya yi shirin korar Fulani daga jihohin Yarabawa


Wata gobara da ta tashi da asubahin ranar Litinin ta kone gidan Sunday Igboho mutumin da yayi barazanar korar al’ummar Fulani daga yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa wasu bata gari da ba a san ko suwaye ba suka cinnawa gidan huta.

A ganawar da ya yi da manema labarai kan batun Igboho ya ce yayi asarar dukiya ta sama da miliyan ₦50 a gobarar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like