Gobara ta kona shaguna 21 a kasuwar yan kifi dake Maiduguri


Wata gobara da ta kama da daren ranar Lahadi a kasuwar kifi dake Maiduguri ta kona shaguna 21.

Mista Ambursa Pindar, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Borno shine ya bayyana haka a Maiduguri ranar Lahadi.

Ya ce binciken farko kan lamarin da hukumar kashe gobarar ta gudanar ya nuna cewa tartsatsin wuta daga daya daga cikin shagunan kasuwar ne ya jawo tashin gobarar.

Ya shawarci yan kasuwar kan suyi kaffa-kaffa wajen yin amfani da kayan masu amfani da wutar lantarki.Inda ya ce ya kamata masu shaguna su rika tunawa suna kashe irin wannan kayayyaki lokacin da suke barin kasuwar.

Pindar ya kuma jaddada muhimmancin ajiye na’urar kashe gobara a shagunans, inda ya ce za su iya amfani dasu wajen kare rayuka da kuma dukiya a duk lokacin da gobara ta kama.


Like it? Share with your friends!

1
79 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like