Gobara ta kona kasuwar yan katako a Jos


Runfuna da basu gaza 100 ne ba suka kone a wata gobara da ta tashi a kasuwar yan katako dake Jos.

Gobarar ta fara ne ranar Litinin da daddare a layin Hausa dake kasuwar ta Laranto a karamar hukumar Jos Norh.

Tashin wuta a kasuwar ta yan katako abu ne da yake faruwa kusan ko wace shekara musamman a lokacin sanyi tsakanin watan Nuwamba da Disamba.

Da yake magana da jaridar Daily Trust,Alhaji Yusuf Aliyu Umar wanda shine shugaban sashen yan katako na kasuwar ya ce gobarar ta fara ne da misalin 11 na dare lokacin da tuni kowa ya rufe shagonsa kuma ta ɗauki kusan sa’o’i biyu tana ci. Ya kara da cewa babu wanda zai iya fadar musabbabin tashin gobarar.

Ya ce duk da cewa jami’an kwanakwana sun yi kokarin wajen shawo kan wutar tuni dukiya ta miliyoyin naira ta kone kafin zuwansu.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like