Hukumar kashe gobara ta jihar Nasarawa tace wata gobara da ta tashi ta kona gidaje shida da kuma kantuna 40 a kan hanyar zuwa Makurdi dake cikin garin Lafiya babban birnin jihar.

Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar, Dogara Dalhatu,  ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN  faruwar gobarar.

Yace gobarar ta faru ne sanadiyar wani tankin ajiye man gas da ya bule yake diga kasa. 

 A kokarin tsayar da zubar da tankin yakeyi,  mai tankin ya kirawo mai walda domin like wurin da yake zuba.

Yace yayin da ake tsaka da aikin ne wutar ta tashi inda ta kona gidaje shida da kuma shaguna 40 dake makotaka da wurin.

Yace duk da dai babu wanda ya rasa ransa a gobarar mutum guda ya samu rauni lokacin da yake kokarin kwaso kayansa daga wani shago.

Dalhatu ya shawarci mutane kan su guji ajiye man fetur a cikin gidajensu.