Gobara ta kashe wasu yara biyu a Kano


Yara biyu ne suka mutu sanadiyar wata gobara da ta kama a wani gida dake Sharada Ja’en Unguwar Yamma a cikin birnin Kano ranar Litinin.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar,Alhaji Muhammad Sa’id ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa yaran da suka rasu na da shekaru hudu da kuma bakwai.

“Mun samu kiran kai daukin gaggawa da misalin karfe 02:09 na tsakar daren ranar Litinin daga wani mai suna,Mallam Bello Tukur dake cewa an samu gobara a wani gida da mutane ke ciki.

“Da samun kiran munyi gaggawar tura motar kashe gobara zuwa wurin da misalin ƙarfe 02:15 na dare domin shawo kan wutar.”ya ce.

Muhammad ya ce iyayen yaran sun fice daga gidan a kokarin neman taimako daga makota lokacin da wutar ta kama amma kokarin kubutar da yaran ya gaza samun nasara.

Ya ce daga baya ma’aikatan kashe gobarar sun kuma mika gawar yaran ga jami’an ƴansanda inda ya kara da cewa tuni suka shiga bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.


Like it? Share with your friends!

3
57 shares, 3 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like