Gobara Ta Ci Gidan Jigon Darikar Tijjaniyya, Sheik Mansur Kaduna


Shugaban Majalisar Malamai Na kugiyar Fityanul Islam Ta kasa Reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, Imam Murabbi Cisse Alyarwawy Ya Shiga Jerin Sahun ‘Yan Uwansa Jagororin Tarikar Tijjaniyya Da Suka Jajantawa Dan Uwansu Shahararran Malamin nan Na Tariqar Tijjaniyya Sheikh Mansur Kaduna Bisa Jarrabawar Gobara Da Allah Ya yi masa Jiya Da Daddare Misalin karfe 2:00 Na Dare A Gidansa Dake Unguwar Kabala a jihar Kaduna.

Na kira Wayarsa Yau Misalin karfe 9:00 Na Safe Don In Jajantamasa Bayan Na Sami Labarin Abinda Ya Faru Wacce Ta Sabbaba Masa Asarar Dukiya Da Littattafa Masu Yawan Gaske.

Sai Ya Daga Wayata Yana Mai kelkelewa Da Dariya Yana Mai Cewa “Shehu Murabbi Ka ji Abinda Mai Kaya Ya yi Da Kayansa Ko” Sai Ya Dawo Shine Mai Jaje Maimakon Shi Za A Jajantawa.

Take Wannan Dariya Tasa Yayin Ibtila’i Ta Tunatar Da Ni wani Hadithin Sayyidina Abdullahi Bn Umara R.T.A Wanda Imamun Nawawy Ya Kawo Shi Cikin Littafinsa (Al Azkaru).

Ga Hadithin Kamar Haka “Abdullahi Bn Umara Ya Binne Wani Dansa Sai Ya kelqele Da Dariya Sai Aka Ce masa Shin Za ka yi Dariya Wajen kabari Sai Yace Ina So ne n Tirmuza Hancin Shaidan”

Tabbas Na san Ba Komai Bane Ya Janyo Wa Dan Uwa Sheikh Ibrahim Mansur Imam Kaduna Wannan jarrabawar Illa Kusancin sa Ga Allah Da Cikar Kamalar Ma’rifarsa.

Allah Ka Bashi Ikon Cin Wannan Jarrabawa, Ka Azurta shi Da Ninke Niken Abinda Ya Rasa Albarkar Maulana Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa A’lihi Wasallama. Wama Zalika Allallahi Bi Aziz.

Comments 3

Your email address will not be published.

  1. Write a comment *innalillahi wa inna ilaihirajuun Allah yky Allah yabashi hakurin jure rashindayay ameen

You may also like