Gobara a sansanonin yan gudun hijira ta raba mutane 371 da matsugunansu a Borno


Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA a jihar Borno ta bayyana cewa matsugunai 140 gobara ta kone a sansanonin yan gudun hijira biyu a karamar hukumar Monguno dake jihar Borno.

Jami’in yada labaran hukumar a shiyar arewa maso gabas,Malam Abdulkadir Muhammad shine ya bayyana haka ranar Lahadi cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.

Ibrahim ya ce an samu faruwar gobarar ne sansanin yan gudun hijira na Flatari da Nguro a Monguno ranar Asabar.

Ya bayyana cewa matsugunai 28 ne suka kone a sansanin Flatari inda ya shafi iyalai 20 yayin da matsugunai 120 suka kone a sansanin Nguro tare da raba iyalai 77 da muhallinsu.

Inda ya kara da cewa a jumlatance mutane 371 gobarar ta raba da matsugunansu a gobarar da ta shafi sansanonin biyu.

Ibrahim ya ce hukumar ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar gobarar tare da gano irin taimakon da suke buƙata.


Like it? Share with your friends!

-1
95 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like