Akalla mutane 255 suka mutu a yayin girgizar kasar da ta faru a gabashin Afghanistan a ranar Talata da daddare. Lamarin ya faru ne a lardin Paktika na gabashin kasar da ke karkashin mulkin kungiyar Taliban. Mutanen yankin sun yi gargadin cewa alkaluman wadanda da ibta’ilin ya shafa ka iya karuwa idan har gwamnatin kasar ba ta yi gaggawar turawa da jami’an da za su yi aikin ceto rayukan mutanen da lamarin ya ritsa da su ba.