Gidaje da shaguna sama da 1000 aka kona a rikicin Kaduna


Wasu mazauna garin Kasuwar Magani dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna sun bayyana cewa akalla shaguna da gidaje da basu gaza 1000 ba aka kona a rikicin da yafaru garin.

Mutane goma sha biyu aka rawaito sun mutu a tashin hankalin da ya samo asali daga rashin fahimta tsakanin matasan Musulmi da Kirista.

Da jaridar The Cable ta ziyarci garin a ranar Talata mutanen garin sun koka kan irin asarar da suka yi.

Mustafa Abubakar ya bayyana cewa an kashe dan uwansa ya yin da aka kona motarsa da kuma shagonsa dake cike da buhun masara 110.

“An kashe dan uwana, an kona mota ta shagonsa dake dauke da buhun masara 110 an kona shi. Ban san abin da zan yi ba.Ban san ta ina zan fara ba a wannan mawuyacin halin,”ya ce.

 Joseph Kwanji ya bayyana cewa asarar dukiyar da ya yi ta kai ta miliyan 10.

Ya ce motarsa kirar akori kura da ya saya miliyan 3.8 a makon da ya gabata ita ma an konata.

Rikicin ya samo asali ne bayan da wata mace kirista ta auri wani musulmi kana ta musulunta al’amarin da bai yi wa yan uwanta da di ba inda suka zo sai sun tafi da ita da karfin tuwo.

Ganin ana ƙoƙarin tafiya da ita ne yasa matasan musulmi suka hana da suka ga anfi karfinsu sai suka koma suka yi gayyar mutane inda daganan rikicin ya barke.


Like it? Share with your friends!

4

Comments 2

Your email address will not be published.

  1. Write a comment *This is unfortunate, We must by all means imbibe the culture oneness and embrace each other. The laws of our land allows everybody irrespective of his religion or ethnic to practice every illegality. We must avoid being driven by our selfish interest in whatever We engage. We need to be caution. I pray the Almighty Allah to prevent the re-occurence of this and any other unwanted destruction of ourselves, our lives and properties no matter on what account. May We continue to live in peace and harmony, ameen.

You may also like