Ghana: Zanga zangar matasa kan gyaran kasa | Labarai | DWSanye da jar taguwa da bakaken wanduna suna rera wakokin kishin kasa, masu zanga zangar sun rika daga kwalaye da aka yiwa rubutu da ke cewa “Cin hanci na haifar da talauci” wasu kuma na cewa “A gyara tsarin Ilmin mu a yanzu”

Matasan sun karade tituna a babban birnin kasar. Zanga zangar ta yau Laraba ita ce ta baya bayan nan tun watan Maris a jerin zanga zangar adawa da gwamnati bayan da kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da yan adawa suka shigar na kalubalantar nasarar sake zabar Akufo-Addo a bara.

Nana Akufo-Addo ya sami nasarar tazarce karo na biyu a karagar mulki da kankanin rinjayen yan majalisar dokoki. Sai dai tun daga wannan lokaci shugaban ke fuskantar matsin lamba yayin da kasar ta yammacin Afirka ta fada matsalolin tattalin arziki wanda ya kara tabarbarewa sakamakon annobar corona.
 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.