Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Atiku Bai Tafi Amurka Ba


An samu rade-radi, muhawara da suka daban-daban a kafofin watsa labarai tun bayanda dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya samu bizar shiga kasar Amurka a makon da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa Atiku wanda ke da muradin ganin ya zama shugaban kasa a 2019, a ranar Alhamis ya bar kasar zuwa Ingila, bayan ya mallaki bizar sa sannan kum cewa ya shirya zuwa Amurka domin kore shakkun abokan adawarsa da suka yi zargin cewa ba zai iya shiga Amurkan ba tare da an kama shi ba saboda rashawa.

A ranar Lahadi, jaridar Thecable ta tattaro daga majiyoyi dalilan da suka sanya Atiku bai tafi Amurka ba kamar yadda aka shirya.

Majiyoyin nasu sun bayyana cewa dawowar Atiku ya kasance saboda kaddamar da kamfen dinsa na shugaban kasa, wanda shi (Atiku) ne uban tafiya, kuma ba zai iya kin halartan wannan taro ba a ranar Litinin.

“Babu shakka zai tafi Amurka amma ba zai yiwu a fara kamfen a bayan idanunsa ba. Hakan zai kasance abun dariya”,inji majiyar.

Wata majiya ma ta bayyana cewa Atiku ya fasa zuwa Amurka ne saboda bai samu tabbacin cewa ba za’a tozarta shi akan zargin rashawa da ake yi masaba wanda akan shi ne aka tsare William Jefferson da Siemens. A koda yaushe yana karyata zargin.

Sai dai daya daga cikin hadimansa ya fada ma The Cable cewa Atiku bai samu zuwa Amurka bane saboda za’a fara kamfen din shugaban kasa na PDP a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba a Sokoto.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like