GARGADI GA MASU SAYEN NAMAN BALANGU, TSIRE, KOSAI KO NAMA.


Mun sani cewar ana nade su (tsire ko balangu) idan mun saya a cikin takardun makarantu ko jaridu.

Yana da kyau mu sani cewar akasarin wadannan takardun ana samo su ne daga dakin ajiye kaya (store) na makarantu.

Wanda a cikin dakin ajiye kayan akwai bera, jaba, kyankyaso, tsaka da sauransu. Suna yin kashi da fitsari a kai, amma haka za a dauko su a kunsa mana gasasshen nama a ciki muna ci.

Hakika wannan babban kuskure ne kuma yana iya haddasa mana cututtuka.

Don Allah a kula!

Allah Ya kara tsare mu.

Kuma yanzu ana fama da wannan cuta ta Lassa, Allah ya kiyayemu baki dayanmu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like