Ganduje ya sanya hannu kan sabuwar doka kafa sabbin masarautu a Kano


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu kan sabuwar dokar kafa masarautu a jihar Kano da majalisar dokokin jihar ta zartar a ranar Alhamis.

Ganduje ya sanya hannu akan dokar a wani dan kwarya-kwaryar biki da aka gudanar a dakin taro na Coronation Hall dake gidan gwamnatin jihar.

An samar da sabuwar dokar ne bayan da wata kotu a jihar ta ce majalisar dokokin jihar bata bi ka’ida ba wajen yin dokar da ta kafa sabbin masarautun.

Da yake jawabi a wurin taron gwamnan ya ce sabbin masarautun da aka samar sun zauna daram babu inda za suje.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like