Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar da majalisar dokokin jihar ta yi wa gyara.

Karkashin sabuwar dokar babu batun karba-karba na shugabancin majalisar sarakuna ta jihar ba kamar yadda yake a kunshin dokar farko da gwamnatin ta samar.

Haka kuma sabuwar dokar ta kara yawan masu zaben sarki daga mutum huɗu ya zuwa mutum biyar a kowace masarauta maimakon huɗu da ake da su a baya.