Ganduje Ya Nemi Janye Karar Da Ya Shigar Kan Dan Jarida Jaafar Jaafar
Gwaman ya shigar da karar ne tun shekara ta 2018, bayan da dan jaridar ya wallafa bidiyon da ya ce gwamnan ne aka nuna yana karbar cin hancin dala miliyan 5.

Gwaman Ganduje dai na tuhumar dan jarida da bata masa suna, wanda hakan ce ta sa ya shigar da karar gaban kotu tare da bukatar kotu ta sa a wanke masa suna, da karyata bidiyo da ya fitar na cewar bayanan ba haka suke ba.

A hirar shi da Muryar Amurka, dan jaridar ya ce gwamanti ta rubutu wa lauyoyinsa wasikar cewar za’a saurari kara ranar shida ga watan gobe, bayan kwana biyu kuma sai suka rubutu cewar zata janye karar da suka shigar. Jaafar ya kara da cewar suna zuba ido har zuwa ranar 6 ga wata su ga shawarar da kotun zata yanke.

Dan jaridar ya kuma kara bayanin cewa, tun da zancen yana kotu ba ya son yin dogon bayani har sai an sake zama kuma kotu ta yanke hukunci, amma tun da farko ya ce zancen a fili ya ke kuma kowa ya ga abinda ya faru, amma abinda ya basu mamaki shi ne yadda mai laifi ke tuhumar wanda bai aikata komai ba da cewar anyi masa kazafi.

Karin bayani akan: Jaafar Jaafar, Nigeria, da Najeriya.

A bangeren lauyoyinsa sun bayyana cewa, suna nazarin al’amari har kafin ranar 6 ga watan inda zasu ji hukumcin da kotu za ta yanke kafin su san matakin da za su dauka.

Da ya ke tsokaci a kan batun, Abbas Yusha’u dan jarida mai zaman kasa ya ce idan har gwaman zai janye, to alamu ne na cewar kila dan jaridar Jafaar ke da gaskiya, ya ce a matsayinsa na dan jarida samun nasarar Jaafar Jaafar shi zai bai wa yan jaridu damar gudanar da aikinsu ba tare da tsoro ba.

A nasa bayanin,masanin harkar siyasa farfesa Kamilu Sani Fagge na Jamia’r Bayero ya ce ba’a san hujjar gwaman ba amma janye karar yana nuna cewar an zo karshen wannan badakalar, amma kuwa sai idan tafiya tayi tafiya ne za’a san manufar gwamanti.

Idan za’a iya tunawa, a kwanakin baya ne dan jaridar ya bar Najeriya sakamakon barazanar da yace yana fuskanta ga rayuwarsa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.