GANDUJE YA KAI ZIYARAR JAJE JIHAR BORNO


Maigirma Gwamna Farfesa Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kai ziyarar taaziyya ga takwaran sa Farfesa Baba Gana Zulum da al’ummar jihar Borno akan manoman da kungiyar Boko Haram suka kashe su 43 a garin Zabarmari dake Maiduguri Jihar Borno.

Farfesa Ganduje ya jajanta tare da nuna alhini akan wannan kisaan gillar ya kuma jagoranci adduo’i akan Allah ya jikan su da rahama Ya kuma kawo mana karshen duk wani tashin hankali a jihar Borno da kasa baki daya.

Farfesa Ganduje ya samu rakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Kano Hon. Abdulazeez Garba Gafasa da kwamishinan yada labarai comrade Muhammad Garba da Maulana Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah da Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare-bari da daraktan kamfen Alhaji Nasiru Aliko Koki da matawallen Kano Alhaji Ali Ibrahim (wakilin Sarkin Kano) da Mai baiwa Gwamnan shawara akan harkokin addinai Alhaji Alibaba A Gama lafiya Fagge da kuma Sheikh Ahmad Sulaiman Ibrahim.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like