Ganduje ya hana Hakimai zuwa Hawan Daushe


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci wasu hakimai dake jihar da kada su halarci bikin Hawan Daushe da Sarkin Kano, Muhammad Sunusi II zai gudanar.

A cikin wata sanarwa,Abba Anwar mai magana da yawunsa ya fitar, Ganduje ya yi kira ga hakiman da su yi murnar bikin sallah a masarautunsu.

Wani sako dake ya wo a kafafen sadarwa na nuni da cewa hakiman da basa karkashin masarautar Kano za su zo a yi bikin Hawan Daushe da su karkashin masarautar Kano.

“Akan wasu kiraye-kiraye dake yawo a kafafen sadarawar zamani dake cewa dukkanin hakimai su halarci Hawan Daushe a fadar mai martaba sarkin Kano. Gwamnatin Kano na umartar dukkanin Hakimai su halarci hawan Daushe karkashin masarautunsu,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa hakiman za su gudanar da dukkanin bukukuwan a karkashin sarakunan su masu daraja ta daya.


Like it? Share with your friends!

1
58 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like