Ganduje ya halarci bikin Maulud a a fadar Sarkin Kano


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci wata tawaga ta manyan jami’an gwamnati ya zuwa wurin Maulidi da aka gudanar a fadar mai martaba sarkin Kano Muhammad Sunusi II.

Shugaban darikar Kadiriya na Afrika ,Shekh Karibulla Nasiru Kabara shine yake jagoran maulidin da aka saba gudanarwa duk shekara.

Ziyarar ta daren Litinin na zuwa ne lokacin da gwamnan ke cigaba da fuskantar suka daga ciki da wajen jihar biyo bayan fefan bidiyon da wata jarida ta wallafa inda aka nuna shi yana karbar kudi daga hannun yan kwangila.

Mutane da dama dai nakira da gwamnan kan ya sauka daga kan mukaminsa kana ya bayar da dama a gudanar bincike.

Sai dai a maimakon ya amsa kiran da ake masa na ya sauka daga kan mukaminsa,Ganduje ya kai kara gaban kotu inda ya zargi jaridar Daily Nigerian da mawallafinta Ja’afar Ja’afar da zubar masa da mutunci da kuma bata masa ya kuma nemi da abiya shi diyar zunzurutun kudi biliyan ₦3.


Like it? Share with your friends!

1
88 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like