Ganduje ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2021


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gabatarwa da majalisar dokokin jihar kasafin kudin shekarar 2021 na biliyan ₦147.9 mai taken Kasafin Kudin 2021 na Farfaɗo da Tattalin Arzikin Da Cigaba Mai Dorewa.

Kasafin wanda ya gaza yawan na shekarar da ta gabata za da za a kashe karin biliyan 14 fiye da na shekarar da ta gabata domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

A kasafin kudin na shekarar 2021 za a kashe biliyan 74.66 wajen ayyukan yau da kullum yayin da bangaren manyan ayyuka zai lashe naira biliyan 73.237.

Za a yi amfani da kudin da aka tara ta hanyar raji da kuma kason da jihar da take samu daga asusun tarayya wajen aiwatar da shi.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 10

Your email address will not be published.

You may also like