GANDUJE YA FIDDA MAKUDAN KUDADE KAN SHIRYE-SHIRYEN SAMAR DA RUGA TA ZAMANI GA FULANI MAKIYAYA A JIHAR KANO


Yau Alhamis, 12 ga watan Satumba, 2019.

Tun bayan wata doguwar tattaunawa da aka yi ta yi a Nageriya kan batun samar da ruga ta zamani ga fulani makiyaya domin inganta tsaron ƙasa gaba ɗaya, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya fidda zunzurutun kuɗi kimanin (Naira Miliyan 300) domin a samar da ɗakunan kwana da sauran abubuwan buƙata ga jami’an rundunar tsaro na sojoji da za su naƙalci dabarun aiki (tirenin) da kuma nome wurin ga fulani makiyaya.

Kamar yadda ya ce: “mun fidda sama da (Naira Miliyan 300) domin a samar da dakunan kwana da sauran kayayyakin buƙata ga jami’an tsaro na sojoji, dan haka, mun samu wurin da sojoji za su dinga gudanar da horon naƙaltar dabarun aiki na dindindin a dajin Falgore. Kuma za mu samar da ƙarin abubuwan buƙata ga fulani makiyaya. Sannan kuma za mu nome wurin ga fulani makiyaya namu.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, ya yin kaddamar da bikin fara ba wa sabbin sojoji kimanin (78) horo na musamman kan dabarun naƙaltar aiki na lafiya wanda aka yi masa take da “Ex Kun Gama” a garin Gada Biyu da ke ƙaramar hukumar Doguwa, Dajin Falgore.

Gwamna Ganduje ya kuma ƙara da cewa “Jihar Kano ta samu zaman lafiya ne a sanadiyyar haɗin kai da ke tsakanin sassan hukumomin tsaronmu. Mun fidda waɗannan kuɗaɗe ayi amfani da su, dan haka mu na fatan maida wannan horon naƙaltar dabarun aiki na sojoji ya zama abu na dindindin. Sannan kuma Fulani makiyaya su samu wurin kiwo mai kyau.

Tare da wannan a wannan wuri, gwamna Ganduje ya kuma yi fatan cewa: “yan bindiga da ɓarayin mutane da ƴan fashi da makami da duk wasu ƴan ta’adda da masu ayyukan laifi ba za su samu mafakar cigaba da ayyukan ta’addancinsu ba a wannan daji”.

Gwamna Ganduje, ya kuma ƙara bayyan haɗin kan jami’an tsaro da kuma sauran al’umma a matsayin wani tsani da ke taimakawa tsaro, duba da yadda ya ga tasirin hakan a Jihar Kano. Kamar yadda ya ce ”

“Na yi farin ciki matuƙa kan wannan horo da za a ba wa sojoji anan, abu ne mai kyau, domin zai taimaka wajen ƙara kyautata dangantaka da fahimtar juna a tsakanin jami’an tsaro na sojoji da kuma sauran al’umma fararen hula”.

Da ya ke gabatar da jawabi, shugaban rundunar sojin ƙasa, Janar Tukur Yusuf Buratai, wanda ya samu wakilcin shugaban sashen sintiri da ba da horo na rundunar soji ta ƙasa, Mejor Jeneral, Onobong Udor, ya bayyana cewa: “samar da ƙarin dangantaka mai kyau a tsakanin rundunar soji da kuma sauran al’ummar garin Gada biyu da na ƙaramar hukumar Doguwa gaba ɗaya, na daga cikin dalilan da su ka sanya shirya wannan taron ba da horo anan.

Dan haka ne ma ya ƙara da jan hankalin al’umma da ka da su ƙi ba wa jami’an soji haɗin kai, musamman ma wajen taimaka musu da bayanan sirri. Waɗanda za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu cikin nasara.

Daga ƙarshe kuma, babban hafsan sojin, Janar Buratai, ya yabawa mai girma gwamna kan lokacin da ya bayar wajen halartar wannan taro.

Kamar yadda ya ce: “Ina miƙa sakon godiya ta musamman ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Gnaduje dangane da lokacinsa da ya ba mu ya kasance tare da mu a wannan wuri da kansa, ba shakka zuwansa ya taimaka matuƙa wajen ƙara ƙayata wannan sha’ani namu na yau”.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like