Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da, Salihu Tanko Yakasai daga mukaminsa na mai bashi shawara na musamman kan kafafen yada labarai.

Mallam Muhammad Garba, kwamishinan yada labarai na jihar shi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

Dakatarwar da aka yi masa bata rasa nasaba da wasu kalaman suka da yayi kan shugaban kasa, Muhammad Buhari game yadda shugaban kasar yake shagulatun-bangaro kan halin da yan kasa suke ciki.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter kan zanga-zangar da ake ta neman a soke rundunar tsaron SARS Yakasai ya kwatanta shugaban kasar da mara tausayi.