Ganduje ya bawa Zainab Aliyu da Ibrahim Abdulkadir tallafin miliyan ₦3 kowannensu


Da yammacin yau ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin,Abike Dabiri-Erewa shugabar hukumar dake kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje a fadar gwamnatin jihar dake Kano.

shugabar hukumar taje Kano inda ta wakilci gwamnatin tarayya wajen mikawa gwamnan Zainab Aliyu da kuma Ibrahim Abdulkadir wadanda gwamnatin Saudiyya ta tsare su.

Zainab da Abdulkadir sun fada hannun hukumomin Saudiyya ne bayan da wasu mutane suka yi musu cushen kwaya a wasu kunshin jakunkuna da aka buga sunansu.

Gwamna Ganduje ya godewa dukkanin mutanen da suka taka rawa wajen sako mutanen biyu musamman shugaban kasa, Muhammad Buhari.

Har ila yau gwamnan ya sanar da bawa kowannensu tallafi kudi na miliyan ₦3.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like