Ganduje ya bada umarnin rufe filayen wasa na Kano gabanin ziyarar Atiku


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin gaggauta rufe manyan filayen wasa biyu dake jihar.

Hakan na zuwa ne kwanaki biyar gabanin ziyarar yakin neman zabe da da dantakarar PDP Atiku Abubakar zai kai jihar.

An shirya gudanar da gangamin yakin neman zaben Atiku ne ranar 10 ga watan Faburairu yayin da shi kuma aikin gyaran filayen za a kammala shi ne ranar 18 ga watan Faburairu.

Wani jami’in gwamnati wanda ya yi magana da jaridar The Cable kuma ya nemi kada a nadi muryarsa ya bayyana cewa an rufe filayen wasannin biyu ne na Sani Abacha da kuma Sabon Gari domin kawo tasgaro ga taron gangamin yakin neman zaben jam’iyar PDP.

Amma mai magana da yawun hukumar wasanni ta jihar,Abbati Bako ya ce rufe filayen bashi da alaka da taron na PDP.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like