Ganduje ya amince Atiku ya yi amfani da filin wasa


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umurnin dakatar da aikin gyare-gyare da ake filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata domin bawa dantakarar shugaban kasa a jam’iyar PDP,Atiku Abubakar damar gudanar da taron gangamin yakin neman zabe.

Gwamnan ya fuskanci suka mai zafi biyo bayan umarnin da ya bayar na rufe filayen wasannin dake jihar domin gudanar da gyara.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar,Mallam Muhammad Garba ya fitar ya bayyana cewa gwamnan ya umarci dan kwangilar da ya kwashe dukkanin kayan aikinsa daga filin har sai bayan jam’iyar PDP ta kammala taron nata.

Sanarwar ta kuma yiwa jam’iyar PDP fatan samun nasarar taron har ila yau ta yi kira da ayi komai cikin tsari dan gudun lalata kayayyaki.


Like it? Share with your friends!

1
74 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like