G7: Karin taimako ga Ukraine | Labarai | DWBirtaniya ta bayyana cewa dole ne a dafa wa Ukraine da karin manyan makamai na yaki, haka da kakaba wasu karin takunkumai kan Rasha, a yayin da ita kuwa Faransa ta bayyana goyon bayan kungiyar NATO face sai Ukraine ta yi nasara a yakin da take da Rasha.

Kungiyar Tarayyar Turai ta da dauki alkawarin bada karin kudade Euro miliyan 500 ga Ukraine. Sai dai da yake mayar da martani a yayin wata ziyarar da ya kai a Tadjikistan, ministan harkokin wajen Rasha Sergueï Lavrov ya zargi tarayyar Turai da kai ruwa rana a rikicin da kasar ta ke da Ukraine.

Rashar dai na cigaba da yi wa Ukraine barin wuta ta sama da kasa, inda ko a wannan Jumma’ar ma’aikatar tsaron kasar ta ce ta kai wasu jerin hare-hare da maiamai masu linzami kan wata matatar mai a yankin Poltava da ke gabashin Ukraine din tare da lalata dumbin runbun tsimi na man fetur.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.