Fitar da N233m: KASCISSIR ta rubuta korafi zuwa ga EFCC a kan Ganduje


Wata kungiya mai rajin kare hakkin jama’ar jihar Kano (KASCISSIR) ta rubuta takardar korafi zuwa ga hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) a kan zargin gwamnatin jihar Kano da fitar da kudi miliyan N233 domin sayen kuri’u a zaben gwamna da za maimaita a wasu mazabu a jihar a ranar 23 ga watan Maris.

A takardar korafin, mai dauke da sa hannun 14 ga watan Maris, da majiyar mu ta gani, KASCISSIR ta bayyana cewar an fitar da makudan kudin ne daga asusun jihar Kano ta hannun ma’aikatar kula da kananan hukumomi.

Kungiyar ta yi zargin cewar gwamnatin jihar Kano ta kasafta kudin zuwa kaso 30, adadin kananan hukumomin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewar za a maimaita zabe a wasu mazabunsu.

“Mun samu bayani a kan fitar da kudin tun ranar 12 ga watan Maris, 2019. Dadi da kari, a ranar 13 ga watan Maris, sai ga shi an kama wasu wakilan APC da su ka amsa da bakinsu a shirin ‘In da ranka’ na gidan radiyon Freedom cewar su na yiwa jam’iyyar aikin sayen kuri’a ne.

“Muna fata hukumar EFCC zata yi bincike a kan wannan korafi tare da daukan matakan ganin cewar ba a yi amfani da kudaden wajen sayen kuri’a kafin ko a lokacin zabe ,” a cewar KASCISSIR.

Sai dai, da aka tuntubi kwamishinan kananan hukumomin jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya yi watsi da zargin cewar an fitar da kudin ne domin sayen kuri’u.

Yace “Tabbas an fitar da kudin kuma an raba su zuwa kananan hukumomi 13 domin kaddamar da wasu aiyuka. Idan aka duba kananan hukumomin da za su ci moriyar kudin za a fahimci cewar zargin da wasu ke yi bashi da tushe balle makama.

“Kananan hukumomin Kumbotso, Kabo, Dawakin Tofa da Tsanyawa na daga cikin kananan hukumomin da su ka samu kaso mai tsoka daga cikin kudin kuma basa cikin wadanda za a maimaita zabe.
“Idan da gaske ne kudin na sayen kuri’a ne da sai mu raba su a tsakanin kananan hukumomi 30 da za a maimaita zabe a wasu daga cikin mazabunsu,” a cewar sa.


Like it? Share with your friends!

-4
89 shares, -4 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like