(Fina-Fina): Adam A. Zango Ya Zama Gwauro Bayan Yin Aure Sau Biyar


Rahoton Mujallar Fim ta watan Yuli-Agusta ta ruwaito fitaccen jarumin Fina-finai Adam A. Zango yanzu a matsayin GWAURO yake, duk kuwa aurensa biyar a baya. Wanda hakan ya sa aka soke shi a matsayin mai auri-saki.

Wanda hakan ya hasala shi ga mayar da martani a wani faifan bidiyo. Jaridar Arewa24news ta gano cewa Zango ya dawo jihar Kano da zama Unguwar Danladi Na Sidi. Ga rahoton da Jaridar Rariya ta taba wallafawa na aurensa sau biyar.

Adam A. Zango Ya Yi Aure A Karo Na Biyar

A ranar Asabar din da ta gabata ne fitaccen jarumin finafinan Hausan nan Adam A. Zango ya sake yin aure, wanda shine karo na biyar da jarumin ya yi aure.

Zango, ya sake yin auren sirrin ne a garin Ngaoudere, dake kasar Kasar Kamaru, inda ya auri a wata mai suna Ummu Kulsum, wadda ake yi wa lakabi da Mama.

Kara auren da Zango ya yi, ya sa yanzu haka yana da mata biyu, inda ya saki uku daga cikin matan da ya aura a baya, wadanda suka hada da matarsa ta farko, wato mahaifiyar dansa na farko, Haidar, da kuma wata da ya auro a garin Lafiayan jihar Nassarawa da kuma wadda ya yi fim din Nas da ita, wadda ita ma ake zaton sun rabu.

Idan ba a mance a kwanakin baya jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyanawa duniya cewa tana matukar kaunar ganin sun yi aure da jarumin, wanda hakan ya sa jama’a suka yi mamakin auren sirrin da jarumin ya yi.

Tuni dai wasu suka soma yi wa jarumin zargin mai yawan aure saki, kasancewar duk da ba wasu shekaru ne da shi sosai ba, amma yanzu aurensa na biyar kenan. Duk da cewa ya musanta cewa shi ba dabi’arsa ba ne auri saki, kawai dai ta sa ce ta fito fili.


Like it? Share with your friends!

3
91 shares, 3 points

Comments 3

Your email address will not be published.

  1. Damankun dauki zango mutumin kirkine aitunda yasaki maryam toh dukwanda ya aurama saiyasaketa insha allah kuzuba idokugani

You may also like