Fayose ya yi hatsarin mota


Toshon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi hatsarin mota akan babbar gadar nan ta jihar Lagos da ake kira Third Mainland Bridge.

Lenre Olayinka, mai taimakawa tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose kan harkokin yada labarai shine ya bayyana haka.

Ya ce Fayose na cikin hayyacinsa kuma yana cigaba da samun kulawa daga jami’an kiwon lafiya.

“Gwamnan jihar Ekiti da ya sauka, Ayodele Fayose ya gamu da hatsarin mota akan gadar Third Mainland Bridge mintoci kadan da suka wuce.Yana cikin hayyacinsa, a yanzu da nake wannan rubutun yana samun kulawa daga jami’an kiwon lafiya,” ya rubuta.

Daga bisani Olayinka ya shedawa jaridar The Cable cewa gwamnan yana jinya a wani asibiti mai zaman kansa.


Like it? Share with your friends!

-3
44 shares, -3 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like