Fasinja ya yanke jiki ya fadi ya mutu a filin jirgin sama na Legas


Wani fasinja mai suna Chukwuma Anthony Eze ya yanke jiki ya fadi ya mutu ranar Laraba a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas.
Wata majiya dake filin jirgin saman ta fadawa kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa fasinjan ya yanke jiki ya fadi ne lokacin da yake jiran kayansa jim kadan bayan dawowarsa daga kasar China.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda dake filin jirgin,DSP Yusuf Alabi wanda ya tabbatarwa da NAN faruwar lamarin ranar Laraba da misalin karfe 09:25 na dare ya ce fasinjan ya sauka ne a jirgin kamfanin Ethiopian Airlines.
A cewarsa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:15 na rana inda aka tabbatar da mutuwarsa a asibitin dake filin jirgin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like