Fashewar bam ta yi sanadin mutuwar mutane 50 a kasar Lebanon


An samu fashewar wani abu da ake kyautata zaton bam ne a birnin Beirut na kasar Lebanon.

Fashewar ta faru ne a tashar jirgin ruwa dake birnin.

Karfin karar fashewar abun ta farfasa gilasan motoci da gidaje a birnin.

Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 50 sanadiyyar fashewar a yayin da sama da mutum 2500 suka jikkata.

Tuni kasar Isara’ila ta musalta cewa tana da hannu a faruwar lamarin.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like