Jihohin sun hada da  Lagos da Oyo da Rivers da Kaduna da Kano da Plateau da kuma Abuja fadar gwamnatin kasar. Mai magana da yawun shugaban kwamitin Willy Bassey ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa, hakan na nufin kara tsaurara matakan hana yaduwar cutar musamman a wannan lokacin da ake fama da sabon nau’inta samfurin Delta.

Wannan gargadin dai na zuwa ne yayin da al’ummar Musulmin kasar ke shirye-shiryen gudanar da shagulgulan Babbar Sallah.