Farashin gangar man fetur nau’in Brent yayi kasa da $40 kan kowace ganga kasa da ma’aunin da Najeriya ta dauka wajen shirya kasafin kudinta na shekarar 2021.

Ya zuwa ranar Alhamis ana sayar da kowace ganga kan kudi dalar Amurka $37.

Hakan na zuwa ne saboda fargabar da ake cewa ƙasashe za su sake saka dokar hana fita ganin yadda cutar Korona ke cigaba da yaɗuwa a kokarin da suke na dakile yaduwar cutar.

Wannan ne farashi mafi sauki cikin watanni.

Najeriya dai ta dogara ne kan manfetur wajen samun kuɗaɗen shiga cigaba da karyewar farashin na iya jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali.