Fadar Shugaban Kasa Ta Nemi Majalisa Ta Gaggauta Dawowa Daga Hutu


Fadar Shugaban kasa ta nemi majalisar tarayya kan ta gaggauta dawowa daga hutun da ta fara don tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban kasa.

Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Majalisa, Sanata Ita Enang ya ce, dogon hutun da majalisar ta fara zai gurgunta harkokin gwamnati musamman ma, batun karin kasafin kudin da Buhari ya gabatarwa majalisar wanda ya kunshi kudaden da hukumar zabe ke bukata don fara shirye shiryen zaben 2019.


Like it? Share with your friends!

-2
87 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like