EU zata tattauna kan sabuwar dokar kasar Hungary | Labarai | DWA cewar wani jami’in kungiyar, batun cecekuce kan sabuwar dokar kasar Hangary din wani babban abun dubawa ne a taron da zai gudana a ranakun Alhamis da Juma’a. Batun dai na zama na gaba-gaba a siyasar Turai a wannan makon biyo bayan matakin Hukumar Kwallon Kafa ta Turai na haramta shirin haskaka filin wasan Munich cikin launukan da ke alamta auren jinsi yayin wasa tsakanin Jamus da kasar Hungary a ranar Laraba.

Fiye da rabin kasashen dake kungiyar ta EU da suka hada da Jamus da Faransa da Italiya da kuma Spaniya ne suka yi wa kasar ta Hungary rubdugu kan sabuwar dokar tare da yin kira kungiyar ta dau mataki da a ganinsu take hakkin ne.

Kazalika kuma ana ganin cewa wannan taron ka iya zama na karshe da shugabar gwamnatin Jamus zata halarta a matsayinta ta shugaba a kungiyar ta EU.
      
    
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.