EU ta gagara sasanta rikicin Balkan | Labarai | DWAn tashi daga taron sasanta Sabiya da Kosovo na wannan Alhamis, ba tare da an cimma matsaya ba. Tarayyar Turai wacce ta kira taron da zummar shiga tsakanin don samar da daidaito a tsakanin makwabtan a birnin Brussels na kasar Beljiyam, ta ce, hakan ba zai sa ta yi kasa a gwiwa ba, saboda haka za a ci gaba da tattaunawar nan gaba.

Sabani a tsakanin yankunan biyu, ya samo asali ne daga takaddama kan mallakar lasisin mota kafin shiga kasar juna, wanda daga bisani ya rikide zuwa tarzoma. A shekarar 1999 Kosovo ta balle daga Sabiya, kafin ta aiyana kanta a matsayin kasa mai cin gashin kanta a shekarar 2008.
 
Leave your vote


Like it? Share with your friends!

-1
66 shares, -1 points

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg