EU na nazarin sabbin takunkumi kan Rasha | Labarai | DW



Matakin kakaba wa Rasha sabbin takunkumin dai bai sami amincewar dukkanin kasashen kungiyar EU ba saboda suna gani  zai Sai cutar da tattalin arzikin kasashensu.

Kungiyar mai mambobin kasashe 27 a baya ta sanya wa Rasha jerin takunkumi har guda shidda tun bayan da shugaba Vladimir Putin ya umarci sojojinsa su afkawa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Bankuna da kamfanoni da kasuwanni har ma da fannin makamashi na jin radadin takunkumin yayin da aka kwace kadarorin jami’ai kimanin 1,200 ko kuma aka hana musu tafiye tafiye zuwa wasu kasashe.

Shugaban kasar Hungary Viktor Orban ya yi kiran a dage takunkumin da kungiyar tarayyar Turai ta sanya wa Rasha yana mai cewa yin hakan shi ne zai sa kasashen su farfado su kuma kauce wa fadawa matsalar koma bayan tattalin arziki.
 




Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg