EndSARS: Lalong Ya Sanya Dokar Ta Ɓaci A Filato


Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya kafa dokar hana fita ta awa 24 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu sakamakon ballewar rikici na zanga-zangar EndSARS a jihar.

Da ya ke yin jawabi a yammacin ranar Talata, gwamnan ya ce dokar hana fitar za ta fara aiki daga karfe 8 na dare har zuwa wani lokaci nan gaba.

Da ya ke tabbatar da mutuwar mutum uku yayin zanga-zangar, gwamnan ya ce saboda haka an haramta duk wata irin zanga-zanga a faɗin jihar gaba ɗaya.

“Bayan samun rahotanni daga hukumomin tsaro da yin nazari kan lamarin, gwamnati ba ta da wani zabi da ya wuce saka dokar hana fita don kare cigaba da asarar rayuka da dukiyoyi.

Na bada umurnin saka dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu daga karfe 8 na ranar Talata 20 ga watan Oktoban 2020 har zuwa nan gaba.

Da wannan umarnin, duk wani nau’in zanga-zanga a kananan hukumomin biyu ya haramta,” in ji shi.

Mista Lalong ya kuma umurci dukkan kamfanoni da ‘yan kasuwa su rufe kasuwancinsu yayin da ya shawarci iyaye su ja kunnen yaransu, matasa don kare rushewar doka da oda.

“Wadanda ke gudanar da muhimman aiki kawai za su fita zuwa wurin ayyukansu,” kamar yadda gwamnatin ta bada umurni. “An bukaci hukumomin tsaro su tabbatar an bi dokar kuma duk wanda aka samu suna saba dokar za a kama su a gurfanarsu da su gaban doka”.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 10

Your email address will not be published.

You may also like