El-Rufai Ya Sokw Dagatai Da Masu Unguwa 390Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya Mallam Nasir Ahmad El-Rufai yace gwamnatinsa ta soke dagatai da masu unguwanni 390 da aka nada a shekarar 2001.

Wata sanarwar da ofishin gwaman ya wallafa a Twitter ta ce an dauki matakin ne domin rage nauyin da kirkirar masarautun dagatan ta yi a kan asusun kananan hukumomin jihar.

A cewarsa, “Yin garanbawul ga gundumomi da kauyukan zai bai wa kananan hukumomi damar gudanar da manyan ayyuka da ci gaban al’umma”.

Gwamna El-Rufai ya kara da cewa yanzu gwamnatinsa ta dawo da tsarin da aka sani gabanin 2011 na dagatai 77 da masu unguwa 1,429.

Ya ce sun dauki matakin ne bayan da suka tuntubi majalisar sarakuna ta jihar, wacce ta bayar da hoton bayanta.”Kirkirar mazabu 313 da aka yi daga shekarar 2001 ta kara yawan dagatai zuwa 390, wanda kuma idan aka hada da ma’aikatansu sun zama 2700 kuma kananan hukumomi ne ke biyansu albashi”, in ji Gwamna El-Rufai.

Ya yi kira ga al’umar jihar su goyi bayan matakin da ya dauka saboda hakan zai inganta ayyukan da kananan hukumomi ke gudanarwa.

A cewarsa, “Kamar yadda muka sha fada a baya, an zabi wannan gwamnati ne domin ta dauki matakai masu tsauri amma masu muhimmanci, wadanda za su rage barnar kudi sai dai za su inganta yadda ake gudanar da ayyuka da mulki a kowanne mataki”.

Comments 0

Your email address will not be published.

El-Rufai Ya Sokw Dagatai Da Masu Unguwa 390

log in

reset password

Back to
log in