El-rufai ya sallami dukkanin masu rike da mukamin siyasa


Gwamnan jihar Kaduna,Malam Nasiru El-rufai a ranar Talata ya sallami dukkanin masu rike da mukamin siyasa a jihar inda ya nemi su mika takardarsu ta barin aiki nan da ranar 30 ga watan Afirilu.

Dukkanin takardar za a tura sune ta hannun sakataren gwamnati na musamman.

Babban mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai Samuel Aruwan shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a jihar.

Ya ce gwamnan na bin damar da kundin tsarin mulki ya bashi na ikon sake mayarsu da kan mukaminsu.

Sanarwar ta shafi dukkanin kwamishinoni, shugabannin hukumomi,manyan sakatarori, mataimaka na musamman, masu bada shawarar da sauran mukamai.

Tuni gwamnan ya umarci ma’aikatar kudi ta jihar da ta tattara alkaluman bayanan hakkinsu na sallama domin biyansu akan lokaci.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like