Ekiti za ta fara biyan ₦30,000 na mafi karancin albashi


Gwamnan jihar Ekiti,Kayode Fayemi ya ce aiwatar da biyan mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar zai fara daga wannan watan.

Ya bayyana haka ne lokacin bikin murnar ranar malamai ta duniya, a Ado Ekiti babban birnin jihar.

An dauki matakin ne domin karfafa gwiwar ma’aikatan da kuma daga darajar ilimi a jihar.

“Zamu fara biyan ₦30,000 ga ma’aikata a Ekiti, farawa daga wannan watan na Oktoba,” ya ce.

Gwamnan ya kara da cewa a kokarinsa na daga darajar ilimi, gwamnatinsa ta bayar da umarnin daukar sabbin malamai 2000.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like