EFCC za ta gurfanar da zaɓaɓɓen gwamnan jihar Bauchi a gaban kotu


Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC ta shirya gurfanar da, Bala Muhammad zaɓaɓɓen gwamnan jihar Bauchi a gaban babbar kotun Abuja.

A takardun shigar da karar da jaridar The Nation tayi tozali da su sun nuna cewa hukumar na tuhumar zaɓaɓɓen gwamnan da laifin karbar na goro ta hanyar karbar wani gida da darajarsa ta kai miliyan ₦550 daga bankin Aso Saving & Loan a shekarar 2014.

Hukumar ta bakin lauyanta,Wahab Shitu ta bayyana cewa zargin karbar na goron da ake zargin tsohon ministan ya aikata.Ya karba ne a matsayin ladan aikinsa.

Zargin da ake zargin Muhammad da shi ya saba da sashi na 18(b) na dokar hukumar hana cin hanci da karbar rashawa ta ICPC ta shekarar 2000 da za iya zartar da hukunci a karkashin sashe na 18(d) na dokar.

Wata majiya ta bayyana cewa za a gurfanar da Muhammad a gobe Litinin a gaban kotun dake Maitama.


Like it? Share with your friends!

2
85 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like