EFCC ta sako Tanimu Turaki


Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta saki Tanimu Turaki babban lauya dake jagorantar karar dan takarar shugaban kasa na jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Turaki wanda babban lauya ne me mukamin SAN an kama shi ne bayan da hukumar ta gayyace shi da ya saka hannu a takardun belin,Babalele Abdullahi sirikin Atiku kuma daraktan dake lura da harkokin kuɗi na rukunin kamfanonin Atiku.

Paul Ibe mai magana da yawun Atiku Abubakar ya tabbatarwa da jaridar The Cable cewa,Turaki shine lauyan dake tsara karar da zata kalubalanci zaben da aka yi wa shugaban kasa Muhammad Buhari.

Jam’iyar PDP tayi zargin cewa kamen na lauyan wani bangare na shirin da gwamnatin Buhari take nayin amfani da hukumomin gwamnati wajen tursasawa yan adawa.

Amma wasu majiyoyi dake hukumar sun sheda wa jaridar cewa Turaki ya amsa tambayoyi ne kan zargin almundahanar kudade har miliyan ₦10 da ake masa.

Ana zarginsa ne da almundahanar kudin lokacin da yake jagorantar kwamitin yiwa mayakan Boko Haram afuwa zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa,Gudluck Jonathan sanda yake rike da mukamin ministan ayyuka na musamman.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like