EFCC ta rufe wasu kadarori mallakin Fayose


Jami’an hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati wato EFFC sun rufe wasu kadarori mallakin tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa kulle kadarorin baya rasa nasaba da umarnin kotu da ta bayar na kwace dukkanin wata kadara da ake zargin an mallaketa da kudin haram.

Hukumar yaki da cin hancin ta gabatar da wasu tuhume-tuhume akan tsohon gwamnan a gaban babbar kotun tarayya dake jihar Lagos bisa zargin aikata almuundahanar kudade lokacin da yake mulki

A wasu daga cikin kadarorin da hukumar ta kwace a birnin Ekiti an rubuta a jikinsu cewa “Wannan ginin ana bincike akansa.”

Fayose ya zargi EFCC da rufe kadarorin mutanen da basu ji ba su gani ba ta hanyar fakewa da cewa mallakinsa ne.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Lere Olayinka ya sanyawa hannu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like