EFCC ta rufe asusun ajiyar gwamnatin jihar Akwa Ibom


Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFFC ta dakatar da asusun ajiyar gwamnatin jihar Akwa Ibom.

Wani babban jami’in gwamnatin jihar shine ya bayyana haka ga jaridar The Cable a jiya Laraba.

Jami’in ya ce gwamnan jihar, Udom Emmanuel da kuma babban akanta na jihar sun kadu matuka da lamarin da yafaru.

“Gwamnan ya kadu lokacin da aka sanar da shi abinda yake faruwa,”a cewar jami’in.

“Ya bukaci karin haske daga hukumar EFCC. Zargin mu shine cewa babban abokin mu da ya sauya sheka shine ya ke da hannu a ciki amma zamu yi yaki da wannan rashin adalci.”

Rufe asusun na jihar ta Akwa Ibom na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da EFCC ta rufe asusun ajiyar gwamnatin jihar Benue.


Like it? Share with your friends!

1
90 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like