EFCC ta rufe asusun ajiyar banki na gwamnatin jihar Benue


Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFFC ta rufe asusun ajiyar banki na jihar Benue.

Terver Akase mai magana da yawun gwmanan jihar shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Makurdi.

Hukumar ta alakanta gwamnan jihar Samuel Ortom da zargin zambar kudade da yawansu ya kai biliyan ₦22 zargin da Ortom ya musalta.

Hukumar ta EFCC ta ce tsakanin 30 ga watan Yuni, 2015 da na watan Maris shekarar 2018 gwamnan ya bada umarnin cire wasu kudade daga asusun jihar dake bankunan GTB, First Bank da kuma bankin UBA.

A rubuce a takarda an yi amfani da kusan biliyan ₦19 na kuɗin wajen biyan hukumomin tsaro shida da aka tura jihar domin shawo kan rikicin manoma da makiyaya.

Amma hukumar ta EFCC tace kasa da da biliyan ₦3 ne na kuɗin aka yi amfani da su wajen biyan hukumomin tsaron sauran kuɗin kuma ba a san me aka yi dasu ba.

Amma gwamna, Ortom ya zargi hukumar yaki da cin hancin da yi masa bita da kulli biyo bayan sauya shekar da ya yi daga jam’iyar APC ya zuwa PDP.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like