EFCC Ta Kwace Gidajen Sanata Saraki Guda Biyar Dake Jihar Lagos


Gidaje a kalla biyar ne a jihar Legas mallakar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ke ci gaba da zama a garkame bayan hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta rufe su.

Ta zarge shi da mallakarsu lokacin yana gwamnan jihar Kwara, “ta hanyar wawure baitul malin jihar domin azurta kansa.”

Sai dai shugaban majalisar dattawan ya musanta zargin, ya ce tuni aka wanke shi a baya, ya kuma bayyana matakin da cewa bi-ta-da-kulli ne kawai.

Sai dai a wata sanarwa da mai bai wa shugaban majalisar dattawan kan harkokin watsa labarai Yusuph Olaniyonu ya fitar ya bayyana cewa, ”matakin da EFCC ta dauka ba wani abu ba ne sai bata sunan shugaban majalisar wanda hakan ya saba dokar Nijeriya.”

Ya kuma bayyana cewa ”hukumar ta dauki wannan matakin ne domin cimma wani buri da ke da nasaba da siyasa kadai.”

Ya tunatar da EFCC cewa gidajen da ake magana a kansu, tuni kotun daukaka kara da kuma kotun koli suka wanke wanda ake zargi.

A karshen makon da ya gabata ne hukumar ta EFCC ta ce tana waiwayen ayyukan shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki a yayin da yake gwamnan jihar Kwara.

Mai magana da yawun hukumar EFCC Tony Orilade ya ce, ” ko ma menene wanda ake zargin bai fi karfin doka ta gayyace shi ko kuma ta gurfanar da shi gaban shari’a ba.”

A yanzu dai hukumar EFCC na bukatar gwamnatin jihar Kwara ta yi mata karin haske dangane da kudin da Sanata Saraki ke karba a lokacin da yana gwamna tun daga 2003 zuwa 2011.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana binciken Saraki kan zargin hada baki da karya ka’idar aiki a ofishinsa da watanda da lalitar gwamnatin jihar Kwara da sata da kuma safarar kudade ta haramtacciyar hanya.

A 2018 ne Saraki ya sauya sheka daga jam’iyya mai mulki ta APC a kasar zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP inda har ya yi takarar shugabancin kasa, sai dai bai kai labari ba tun a zaben fitar da gwani.

Daga baya kuma ya yi takarar sanata a jiharsa ta kwara inda a nan ma bai samu nasarar lashe zaben ba.


Like it? Share with your friends!

-1
80 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like