EFCC ta kama dan uwan sakataren gwamnatin Zamfara dauke da miliyan ₦60 da bindiga


Hukumar efcc mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati, shiyar Sokoto a ranar Talata ta kama wani mutum mai suna Murtala Muhammad dauke da kudi naira miliyan 60.

Hukumar ta samu wannan nasarar ne bayan bayanan sirri da ta damu cewa ana zarginsa da halasta kudaden haram.

Mutumin da ake zargi dan uwane ga sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Abdullahi Shinkafi.

Sauran kayan da aka samu a wurinsa sun hada da mota kirar Prado Jeep, karamar bindiga kirar gida dauke da harsashi.


Like it? Share with your friends!

1
102 shares, 1 point

Comments 7

Your email address will not be published.

You may also like